Rundunar sojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kubutar da wasu mutane 212 daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram, lokacin da suka kai sumame wasu kauyuka da ke makwabtaka da dajin sambisa, inda suka samu kuma nasarar kakkabe mayakan da ke zaune cikin kauyukan.
Wata sanarwa da kakakin rundunar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya fitar yau, ta bayyana cewa rundunar ta samu nasarar cafke daya daga cikin jagororin kungiyar mai suna Amman Judee inda suka kashe hudu daga cikin mayakan.
Birgediya Janar Kukasheka ya kuma ce yanzu haka rundunar ta fara binciken wanda suka cafken, wadanda kuma aka samu nasarar ceto su an killace su wuri guda, inda aka gudanarwa kananan yaran da ke tare da su allurar rigakafin polio.
Rahotanni sun bayyana cewa wannan shine karo na biyu a cikin sati guda da rundunar sojin najeriya ta samu nasarar ceto mutane daga hannun mayakan kungiyar Boko Haram, wadanda adadin su ya tasamma dari biyu da arba’in da biyu.
A ranar asabar ne rundunar ta ceto wasu mutane 30, inda suka samu nasarar kashe mayakan kungiyar goma sha daya a wasu kauyuka takwas da su ka kai sumame da ke yankin karamar hukumar Bama.
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin mutane dubu dari ne suka rasa rayukan su tun bayan billowar rikicin mayakan Boko Haram tun daga shekarar 2009 zuwa yanzu.