Day: May 10, 2019

Daurawa ya ajiye mukaminsa na shugaban Hisba

A yau juma’a ne 10 ga watan Mayu 2019 shugaban hukumar HISBA ta jihar Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa ya mika takardar ajiye aiki daga shugabantar hukumar ga gwamnatin jihar Kano. Takardar ajiye aikin wadda hadimin Sheikh Ibrahim Daurawa din, Malam Umar Muhammad Tukur ya mika takardar ajiye aikin a ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano. […]

Kotun daukaka kara ta soke karar da Onnoghen ya shigar gabanta

Kotun daukaka kara dake Abuja ta soke daukaka karar da dakataccen babban jujin kasar nan Walter Onnoghen ya shigar gaban ta. Kotun ta ce karar an rigaya an saurare ta a kotun da’ar ma’aikata kuma tuni ma da aka kammala sauraran ta a kotun. A yayin da ake yin shari’ar karkashin jagorancin mai shari’a Stephen […]

Shugaba Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaro su kara jajircewa akan aikin su

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya bukaci manyan hafsoshin tsaron Najeriya da su kara jajircewa wajen tabbatar da cikakken tsaron rayuka da dokiyoyin al’umma. Muhammadu Buhari na wadannan kalaman ne lokacin da yake ganawa da manyan hafsojin tsaron  a fadar Asorok da ke birnin tarayya Abuja. Shugaban kasar ya kuma bukaci sufeto janar na ‘yan sandan […]

Hukumar NRFF ta nada Yaro a matsayin sabon mai horaswa

Hukumar wasan kwallon Rugby ta Najeriya NRFF ta nada Abubakar Yakubu wanda aka fi sani da Yaro a matsayin sabon mai horas da kungiyar. A cewar shugaban hukumar kwallon Rugby na kasa Kelechukwu Mbagwu an nada Abubakar Yakubu ne da nufin bunkasa kungiyar. Kelechukwu Mbagwu ya ce kwarewar da tshohon dan wasan Rugby Abubakar Yakubu […]