Day: May 17, 2019

Gwamnatin tarayya ta karawa masu hidimar kasa alawus zuwa 30,00

natin tarayya ta kara alawus din wata-wata na masu yiwa kasa hidima zuwa dubu talatin. Ministar kudi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka yayin taron manema labarai jiya a Abuja. Ta ce gwamnati tana tsara yadda za ta fara biyan naira dubu talatin a matsayin alawus da ta ke bai wa masu yiwa kasa hidima. […]

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama masu garkuwa da mutane 93

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce, takama masu satar mutane suna garkuwa da su a yankin arewacin Najeriya guda 93. Mai magana da yawun rundunar DCP Frank Mba ne ya bayyana haka lokacin da ya ke holin batagarin a kauyen Katari da ke kan titin Kaduna zuwa Abuja. Ya ce jami’an Operation Puff Adder ne […]

Gwamnatin tarayya zata baiwa jihohi kudaden Paris club

Gwamnatin tarayya ta ce nan bada dadewa ba, za ta bai wa jihohi kason karshe na kudaden Paris Club da ya kai sama da naira biliyan dari shida da arba’in da tara. Ministan kudi Zainab Ahmed ce ta bayyana haka yayin wani taron manema labarai jiya a Abuja Ta ce tuni ma’aikatar kudi ta kammala […]