Day: May 29, 2019

Gwamna Ganduje kara mayar da wasu kusoshinsa kan mukamansu

Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sake nada Alhaji Usman Alhaji a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar ta Kano. Haka zalika gwamna Ganduje ya kuma ce, Alhaji Shehu Mu’azu, ya ci gaba da kasancewa a mukamin akanta Janar na jihar Kano Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Abba […]

NUT ta bukaci Mhummadu Bahari ya kara kokari kan mafi karancin albashi

Kungiyar malamai ta kasa NUT ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi duk me yiwuwa wajen ganin an aiwatar da tsarin mafi karancin albashi ga dukkannin ma’aikatan tarayya, jihohi da kananan hukumomi. Sakataren yada labarai na kungiyar, Titus Amna ne ya bayyana haka ga manema labarai yau a Abuja. Mr Titus Amba ya […]

kwalejin fasaha ta kano: za mu kara kaimi wajen bunkasa harkokin ilimi

Kwalejin fasaha ta Kano ta bayyana aniyarta ta kara kaimi wajen bunkasa sha’anin koyo da koyarwa  ga dalibai. Shugaban kwalejin Farfesa Mukhtar Atiku Kurawa ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a kwalejin. Ya ce matakan da suka dauka sun hadar da tantance kwasa-kwasai da ake koyar dasu domin a yarda da su […]