Day: July 5, 2019

An sake nada Abba Kyari matsayin shugaban ma’akatan fadar gwamnati

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Abba Kyari a matsayin shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa. Haka zalika Muhammadu Buhari ya kuma amincewa Boss Mustapha, ya ci gaba da kasancewa a matsayin sakataren gwamnatin tarayya. Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan […]

Gwamnatin Jihar Gwambe tayi kan matakin Gwamnatin tarayya

Gwamnatin jihar Gombe ta bayyana rashin jin dadin ta kan matakin gwamnatin tarayya na dakatar da shirin samar da wuraren kiwo da kuma tsugunar da makiyaya a wasu jihohin kasar nan. Gwamnan jihar Alhaji Inuwa Yahaya ne bayyana hakan lokacin da yake ganawar da manema labarai, jim kadan bayan wata ganawar sirri da shugaban kasa […]

JAMB yayi zargi kan zanga zangar adawa da ayyukan hukumar

Shugaban hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta kasa JAMB Farfesa Is-haq Oloyede yayi zargin daukar nauyin zanga-zangar adawa da ayyukan da hukumar ke aiwatarwa. Is-haq Oloyede ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi ga manema labarai yau a birnin tarayya Abuja, tare da bayyana sunan wani dalibi da hukumar ta kwce sakamakon jarrabawar […]

Gwamnatin tarayya ta bayyana kudaden da ake kashewa wajan shigo da madara

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa adadin kudaden da ake kashewa duk shekarar wajen shigo da madara da dangogin ta daga ketare ya tasamma Dala Biliyan daya da miliyan dubu dari uku. Babban sakatare a ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya Dakta Mohammed Umar ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin babban taron […]

Tsofaffin Shugabanin Kwamin riko sunyi karar Gwamnan Bauchi

Tsofaffin Shugabannin kwamitin riko na kananan hukumomin jihar Bauchi guda Ashirin sun gurfanar da gwamnan jihar Sanata Bala Muhammed gaban kotu bisa zargin sa da sallamar su batare da wa’adin su ya cika ba. Tsohon shugaban kwamitin riko na karamar Hukumar Bauchi Alhaji Chindo Abdu ne ya bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a […]