Gwamna Yari na yaki da batun karin mafi karancin albashi domin kare kuskuren sa

Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ta kasa NULGE ta ce gwamnan jihar Zamfara Abdulazeez Yari na yaki da batun karin mafi karancin albashi ne domin kare kuskuren da ya tafka na kin biyan ma’aikatansa mafi karancin albashi na naira dubu 18 da ya yi.

Shugaban kungiyar ta kasa Kwamared Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan ga manema labarai, inda ya ce ma’aikata a jihar Zamfara na daukar naira dubu shida ne kawai a matsayin mafi karancin albashi.

Ya kuma ce mafiya yawan tashin hankulan da ke faruwa a jihar Zamfara na da nasaba da karancin kudaden da ma’aikatan ke dauka a matsayin albashi.

Kwamared Ibrahim Khalil ya ce matukar ma’aikata basu samu kudaden da ya da ce da za su iya kula da kan su ba, shakka babu, ba tayyada za a samu zaman lafiya a jihar.

Ya kuma koka kan yadda ma’aikatan jihar Zamfara suka zama koma baya a kasar nan ta fuskar kula da walwalar su, inda ya ce a jihar filato baya ga naira dubu 18 da ta ke biya a matsayin mafi karancin albashi, su kan su kananan hukumomin na karawa ma’aikatan su dan wani abu.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO