Kano:Majalisar dokokin jihar ba ta da ikon bincikar Gwamna Abdullahi Ganduje

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

A yau Alhamis ne babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin cewa majalisar dokokin jihar Kano ba ta da iko, ko hurumin gayyata ko kuma bincikar gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje kan zargin karbar na goro a hannun ya kwangila.

 

Kotun karkashin jagoranci mai shari’a Ahmad Tijjani Badamasa ta yanke hukuncin cewa ikon bincikar manayan laifuka na wuyan hukumar Yan Sanda ne ko kuma hukumar EFCC ko ICPC.

 

Mai shari’a A T Badamasi ya ce ikon da tsarin mulkin kasa ya bawa majalisar dokokin jiha, shi ne kawai su samar da doka su kuma tabbatar da doka na aiki, amma basu da ikon bincikar manyan laifuka.

 

Jim kadan bayan yanke hukuncin ne lauyan wadanda suka shigar da kara Barrister Nuraini Jimoh ya yaba da kokarin kotun na yanke hukuncin, inda kuma lauyan wadanda ake kara Barrister Muhammad Waziri ya ce zai tattauna da wadanda ya ke karewa domin daukar mataki na gaba.

 

Wakilin mu Muhammad Bashir Inuwa ya ruwaito wadanda ake karar sun hadar da majalisar dokokin jihar Kano da kuma shugaban kwamitin binciken na majalisar Baffa Babba Danagundi ta kuma attorney janar na jihar Kano.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO