Shugaba Buhari ya dawo gida bayan halarta taron dumamar yanayi na COP24 a kasar Poland

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan halartar wani taron majalisar dinkin duniya kan dumamar yanayi mai taken: ‘’’COP24’’ a birnin Kotowice da ke kasar Poland.

 

Yayin taron na kwanaki goma sha biyu, shugaban kasar ya kuma gabatar da jawabi tare da tattaunawa da wasu shugabannin kasashen duniya da kuma al’ummar kasar nan mazauna kasar ta Poland.

 

Wasu daga cikin shugabannin kasashen duniyar da shugaba Buhari ya zanta da su, sun hada da: Alain Berset na kasar Switzerland da Andrzej Duda na kasar Poland da kuma shugaba Alexander Van der Bellen na kasar Austria.

 

A shekaran jiya talata ne kuma shugaba Buhari ya ziyarci gidan ajiya kayan tarihi na mutanen da suka rasa rayukansu a yakin duniya na biyu da ke Oswiecim.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO