Jam’iyyar APC ta sanya Aliko Dangote Femi Otedola cikin shawarwarin yakin neman zaben shugaba Buhari

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Jam’iyya mai mulki ta APC ta sanya fitattun ‘yan kasuwar nan Alhaji Aliko Dangote da kuma Femi Otedola cikin mambobin kwamitin bayar da shawarwari nay akin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wannan na kunshe a wata sanarwa da mashawarcin shugaban kasa Muhammadu Buhari na musamman kan al’amuran yada labarai, Mr Femi Adesina ya fitar yau Juma’a a Abuja.

Sauran mambobin kwamitin sun hadar da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da jagoran jam’iyyar ta APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da Sanata Ahmed Lawan, da Femi Gbajabiamila da kuma shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomole.

Ta cikin sanarwar Femi Adesina ya kuma bayyana cewa jam’iyya mai mulkin ta APC ta fitar da sunayen mutanen da za su kawo mata shawarwari kan yakin neman zaben, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci kwamitin, yayinda Bola Tinubu kuma zai kasance shugaban kwamitin na biyu.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO