Ana dakon abinda ka iya faruwa sakamakon cikar ritayar babban sefeton yan sandan kasar nan

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

A yanzu haka ana dakon abin da ka iya kasancewa a cikin rundunar yan sanda ta kasa, sakamakon kammalar lokacin ritayar babban sefeto yan sandan kasar nan Ibrahin Idris a yau.

Ibrahim Idris wanda shine sifeton yan sandan kasar nan na goma 19, ya samu mukamin ne bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nadashi a ranar 21 ga watan maris din shekarar 2016 da ya karbi SolomArase.

Rahotanni sun bayyana cewar ya iso lokacin ritayar sa ne biyo bayan cika shekaru 35 yana aiki, sai dai wasu zantuka na kewayawa da ke rade-radin shugaban kasa Muhammadu Buharu zai kara masa wa’adi tun da dai bai cika shekara 60 a duniya ba.

Sai dai tuni al’umma suka fara sukar batun kara wa’din ga babban sifeton yan sandan, inda kuma suka ce suna dakon abin da zai faru kan batun babban sifeton nan da awannin 24

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO