Kungiyar kwadago zata cigaba da ganawa da gwamnatin tarayya

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Kungiyar kwadago zata ci gaba da ganawa da gwamnantin tarayya a yau litinin kan batun mafi karancin albashi bayan ganawar da suka yi a ranar juma’ar da ta gabata, wanda aka tashi taron ba tare da an cimma wata matsaya ba.

Kungiyar kwadagon dai na bukatar fadar shugaban kasa ta mika kudurin dokar mafi karancin albashi gaban majalisun tarayyar kasar nan don mayar da shi doka.

Jim kadan bayan kammala taron da kungiyar ta kudanar da gwamnantin tarayya a ranar juma’ar da ta gabata shugaban kungiyar na kasa Ayuba Wabba ya shaida cewa kungiyar zata kuma zama da gwamnantin tarayya a yau litinin.

Ya kuma kara da cewa zasu yi ganawar ta yau ne da misalin karfe 5 na yamma, inda yace badon shirin tattaunawar ba, kungiyar ta shirya tsunduma yajin aiki a yau.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO