Tsohon mai shariah Mamman Nasir ya tsallake rijiya da baya a jiya

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Tsohon shugaban kotun daukaka kara Galadiman katsina kuma hakimin Karamar Hukumar Malumfashi Mai Shari’a Mamman Nasir ya tsallake rijiya da baya a jiya litinin daga hannun masu garkuwa da mutane.

Rahotanni sun bayyana cewa mai shari’a Mamman Nasir ya yi nasarar dawowa gida cikin gigita, sai dai kuma masu garkuwa da mutanen sun sace mai tsaron lafiyar sa wanda aka bayyana sunan sa da Aminu.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya faru ne a jiya litinin da misalin karfe 9 da rabi na safe, a tsakanin kauyen Gora zuwa Yammawa da ke kan hanyar Malumafshi a cikin karamar hukumar Malamumfashin jihar Katsina.

An kuma gano cewa masu garkuwar sun tare hanyar wucewar motoci, tare da tsare su, suka kuma rika leka motocin suna neman wanda zasu sace anan ne kuma suka ganshi, inda suka yi yunkurin dauke shi amma ya yi nasarar tserewa.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lokacin da suka gano shi, ne ya yi saurin ficewa daga motar sai dai mai tsaron lafiyar sa baiyi saurin fita ba al’amarin da ya basu damar tafiya da shi zuwa wani daji dake kusa.

Bayan faruwar al’amarin ne dai masu jaje suka rika tururuwar zuwa yi masa jaje amma dai an gano cewa ya roke su da su bashi damar hutawa don kuwa har yanzu jikin shi na rawa. Sai dai kuma duk kokarin da aka yi na jin ta bakin kakakin yan sandan jihar SP Gambo Isa amma hakan bai samu ba

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO