Yan fashi sun kaiwa shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Benue hari

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

A jiya Talata ne Yan fashi suka kaiwa shugaban kungiyar yan kwadago ta kasa reshen jihar Benue Godwin Anya hari a dai-dai lokacin da kungiyar ke gudanar da zanga-zangar tilastawa fadar shugaban kasa ta aikewa da majalisun tarayyar kasar nan kudurin dokar mafi karancin albashi don mayar da ita doka.

Sai dai kuma ya tsallake rijiya da baya a lokacin da suka kawo masa, amma dai sun harbi matar sa.

Anya da iya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho, inda ya tabbatar da cewa harin ne ma ya hana shi halartar taron zanga-zangar da suke aka gudanar a jiya Talata.

Ya kuma kara da harbin matar sa da aka yi ne ya hanashi jagorantar zanga-zangar.

Sai dai kuma hakan bai hana sauran shugabannin kungiyar gudanar da zanga-zangar da suka mamaye manyan titunan babban birnin jihar Makurdi.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO