An rantsar da mai shari’a Uwani Musa Abba Aji a matsayin shugabar kotun kolin kasar nan

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Babban jojin kasar na mai shari’a walter Onnoghen ya rantsar da mai shari’a Uwani Musa Abba Aji a matsayin shugabar kotun kolin kasar nan bayan da ta shafe shekaru 14 tan jagorantar kotun daukaka kara.

An dai rantsar da ita ne a kotun kolin da ke babban birnin tarayya Abuja.

A yayin bikin rantsuwar dai babban jojin kasar nan ya yi kira gareta da ta yi aiki tukuru cikin gaskiya da rikon amana don ciyar da harkokin shari’a gaba a kasar nan.

Ya kuma kara da cewa ranstuwar tata na zuwa ne a dai-dai lokacin da kotun kolin ta cika da shari’o’I a don haka ya kamata ta zage damtse.

Daga nan kuma sai ya yi kira ga kafatanin alkalan kasar nan da su rike gaskiya a yayin gudanar da aikin su yadda ya kamata, inda yace ya zama dole ko wane alkali ya zo aiki cikin shirin fuskantar kowane irin kalubale.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO