Yan sanda sun garkame ofishin dakatancen babban jojin kasa

Da safiyar yau Litinin ne Jami’an ‘yasanda sun garkame ofishin dakatancen babban joji na kasa mai shari’a Walter Onnoghen dake babban birnin tarayya Abuja.

 A ranar Juma’ar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da bbabn mai shair’a na kasa Walter Onnoghen daga mukamin sa.

Wata majya daga kotun koli ta bayyana hakan ga manema labarai cewa jami’an sun hana shige da fice a harabar ofishin.

A cewar su wannan mataki ne na hana babban mai shari’a na kasa shiga ofishin yayin da suka umarci dukkannin jami’an dake gudanar da aiki a ofishiin da su fice ba tare da bata lokaci ba.

Majaiyar ta ce Jami’an ‘yan sandan sun je ofishin ne da misalin karfe 7 na safiyar yau Litinin.

Hakan ya biyo bayan taron gaggawa da majalisar kula da harkokin shari’a ta kasa ta ce zata yi a gobe Talata kan dakatar da babban mai shari’ar na kasa Walter Onnoghen.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO