Ministan kasafi:Ana sa ran tattalin arzikin Najeriya zai karu da sama da kashi 3

Ministan kasafin kudi  da tsare-tsare na Najeriya, Udoma Udo Udoma ya ce, akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar zai karu da fiye da kashi uku a bana kamar yanda  wani rahoton Asusun bayar da  lamuni na duniya, IMF ya fitar.

Udo Udoma ya ce rahoton da IMF ya fitar Ya bayyana yanda tattalin arzikin kasar nan a watan junairun da ya gabata ya yi sama musamman ta bangaren kasuwar danyen mai  ya karu da sama da Kashi biyu.

 Udoma ya kara da cewa   Ana saran kasafin kudin bana zai habaka tattalin arzikin kasar nan tare da samarwa  matasan ayyukan yi a kasar nan, baya ga ragewa da yawa daga cikin al’umma halin matsin da suke ciki.

A cewar Minista Udo udoma a dadin da ake sa ran za’a samu ya kai sama da kaso tara a shekarar nan, daga cikin kaso goma sha daya hkamar yadda yake a karshen shekarar 2018.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO