0 Comments

Dan gidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, Olujonwo Obasanjo ya cigaba da yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari gangamin yakin neman zabe a kasar Amurka.

Olujonwo Obasanjo, wanda shi ne shugaban kungiyar matasa masu yakin neman zaben  shugaba, ya ce ya je kasar Amurka ne don neman goyan bayan ‘yan Najeriya mazauna kasar domin sake zaben shugaban  Muhammadu Buhari.

Dan son  tsohon shugaban kasar yayi bayanin cewa, dalilan da suka sanya yake neman goyan bayan da a zabe shugaban kasar shi ne, kasancewar a yayin mulkin sa ya maida hankali kan samawa dimbin matasa aikin yi, yayin d aya saita Najeriya kan turbar da ta dace.

Har’ila yau,Olujonwo Obasanjo ya ce yana goyan bayan shugaban kasa saboda yadda gwamnatin shugaban kasar ta tsaya kai-da-fata kan bunkasa ilimi da karfafawa matasa gwiwa,a don haka yake yakin neman zaben Muhammadu Buhari.

Share
Share
Language »