Kungiyar boko haram ta kai hari karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa

Kungiyar Boko Haram ta kai hari kan al’ummar karamar hukumar Madagali dake jihar Adamawa a daren jiya Litinin, yayin da suka tarwatsa ‘yan sanda dake kan aiki, da kuma tada hargitsi a cikin garin.

Wani jami’In tsaro da ya nemi a saka sunan sa, ya bayyana wa manema labari  da safiyar yau cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun kashe mutum 3, da lalata shaguna 20 da motoci 3 yayin da suka kwashe kayayyakin abinci.

Jami’in tsaron ya ce daga cikin yankunan da abun ya shafa akwai Shuwa da Kirshingari da kuma Shuari.

Sai dai kwamandan rundunar ta 28 dake Mubi Lut Kanal Haruna ya ce tuni sojojin kasar nan suka maida martani kan harin

Yayin da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa Othman Abubakar ya bada tabbacin cewa tuni hukumomin tsaro suka maido da zaman lafiya a yankin.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO