‘Yan gudun hijira sun gudanar da zanga-zanga sakamakon yunwa da ta addabe su

A jiya Taalata ne dubban ‘yan gudun hijira da ke Baga a garin Maidugurin Jihar Borno suka mamaye manyan titinan dake garin domin nuna damuwar su bisa rashin kayan abinci da suke fuskanta.

Haka kuma rahotonni sun yi nuni da cewa zanga zangar ta hadar da rashin magunguna da kulawa da basa samu a yayin da basu da lafiya a sansanin da suke zaune.

Masu zanga zangar sun rufe wasu manyan tituna a garin na Maiduguri da suka hadar da babban titin Maiduguri zuwa Kano da sauran wasu muhimman hanyoyi.

Zanga-zangar ta hadar da mata da kananan yara maza da mata da maza da suka fito dauke da kwalaye dake dauke da rubutu da ke nuna irin matsalar da suke fuskanta tare da rera wakoki na irin matsalolin da ke damun su.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO