Walter Onnoghen:ya kalubalanci rashin cancantar alkalin kotun da’ar ma’aikata

Dakataccen babban jojin Najeriya Walter Onnoghen ya kalubalantar rashin cancantar alkalin kotun da’ar ma’aikata Danladi Umar wajen cigaba da shari’ar, da ake masa kan zargin bayyana kadarorin da ya mallaka

A jiya ne lauyoyin da suke kare Walter Onnoghen suka nemi  Danladi Umar  da ya janye daga cigaba da gabatar da karara a matsayin sa na alkalin kotun da’ar ma’aikata saboda zargin karbar na goro na Naira miliyan 10 da hukumar EFCC ke yi.

Karar mai dauke da sa hannun Chris Uche mai darajar SAN da Chief Sebastine Hon mai darajar SAN da Okon Efut da Chief Ogwu Onoja mai darajar SAN da Noah Abdul da George Ibrahim.

Lauyoyin sun nemi Daladi Umar da ya janye daga cigaba da gabatar da karar saboda rashin cancatar sa

Dakataccen baban jojin kasar ya bayyana Danladi Umar da cewa bashi da aniyya mai kyau, kuma shi ne mai gabatar da karar kuma shi ne alkali a gefe guda kuma shine mai kare wanda ake gabatar da kara.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO