INEC:baza mu daga zabe don canza ‘yan takara ba

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta ce ba za ta daga lokutan zabe ba biyo bayan umarnin da kotunan kasar nan suka bayar na maye guraban wasu yan takarar da wasu.

Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakube ne ya sanar da hakan ya yin zauren masu ruwa da tsaki kan shirin gudanar da zabe na bana da hukumar ta shirya aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Ya cu hukumar ta na ta karbar umarni da ga kotuna daban-daban na musanya wasu yan takarar da wasu, yayinda wasu umarnin ma ke cin karo da juna.

Ya kuma ce humar ta INEC tana aiki ne da abin da ya zo mata na karshe don haka bata bukatar wani al’amari da zai dauki lokaci.

Farfesa Yakubu ya kuma ce zaben fidda gwani da jam’iyyun suka gudanar a wannan karon shi ne mafi rudani da aka taba samu a Najeriya tun bayan dawowar mulkin dimukuradiyya Najeriya a shekarar 1999 inda hukumar ta INEC ta karbi hukuncin kotu har 640.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO