Bill Clinton zai halarci taron sanya hannun yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan ’takarar Najeriya

Kwamitin wanzar da zaman lafiya tsakanin ‘yan takarar Najeriya, ya ce ana saran  tsohon Shugaban kasar Amurka Bill Clinton zai halarci taron  sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin ‘yan ’takarar shugabancin kasar nan karkashin inuwar jama’iyar APC, Muhammadu Buhari da kuma takwaransa na jam’iyyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kwamitin wanzar da zaman lafiyar, Atta Barkindo, ya ce, taron zai gudana ne a jibi laraba a babban dakin taro na kasa da kasa da ke birin tarayya Abuja.

Ya kuma ce, babban sakatariyar kungiyar kasashen rainon Ingila, Baroness Patricia Scotland, za ta halarci taron, a inda bayan kammala taron sanya hannu kan yarjijeniyar zaman lafiyar, Bill Clinton zai gana da yan’takarar jami’yyun guda biyu.

Atta Barkindo, ya kara da cewa, a yayin babban zaben Najeriya da ke karatowa ya zama wajibi al’umma su san mahimmancin zaman lafiya a tsakaninsu, tare da kauracewa rigingimu a tsakanin matasan kasar nan musamman a lokacin zabe da kuma bayan zaben.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO