Rundunar ‘yan sanda za ta girke jami’anat a ofisoshin hukumar INEC

Mai rikon mukamin Sifeto janar na ‘yan sandan Najeriya Muhammed Adamu, ya bada umarnin rarraba ‘yan sanda a ofisoshin hukumar zaben mai zaman kanta ta kasa INEC da ke fadin kasar domin tabbatar da tsaro a yayin babban zaben da ke tafe.

Muhammed Adamu ya kuma ce, ya zama wajibi duk wasu kwamishinonin ‘yan sanda da ke fadin Najeriya su tabbatar da cewa sun bada cikakken tsaro a jihohin su ta hanyar kula da ofisohin hukumar zaben da kuma kayan aikin da aka kawo domin gudanar da zaben yadda ya kamata.

Ya ce ya zama wajibi duk wani jami’in Dan sanda da ke kula da tsaron al’umma a yayin zaben da ya rika kula da yadda harkokin tsaron ke gudana, kuma da zarar sun samu wata matsala su sanar da ofisoshin yan’sanda da ke kusa dasu.

Muhammed Adamu ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su kwantar da hankulan su tare da basu hadin kai a yayin da suke   gudanar da ayyukan su a lokutan zabe.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO