Hukumar EFCC ta kama Babachir David Lawal bisa zargin cin hanci da rashawa

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta kama tare da tsare tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir David Lawal game da zargin badakalar cin hanci da rashawa.

Haka kuma an ce a yau Talata ake saran hukumar ta EFCC za ta gurfanar da Babachir David Lawal gaban kotu.

Sauran wadanda hukumar ta EFCC za ta gurafanar tare da Babachir David Lawal sun hada da: Hamidu David Lawal da Sulaiman Abubakar da Apeh John Monday da kuma kamfanonin Rholavision Engineering Limited da Josmon Technologies Limited.

Rahotanni sun ce hukumar ta EFCC za ta gurfanar da sune gaban babbar kotun birnin tarayya Abuja kan zargin su da badakalar sama da naira miliyan dari biyar da arba’in da hudu na kwangilar cire ciyawa.

A cikin kunshin takardar karar da lauyoyin hukumar EFCC Offem Uket da M.S. Abubakar da kuma Abba Muhammed suka shigar gaban kotun sun zargi Babachir David Lawal da ba da kwangila ga kamfanin sa.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO