Kungiyar matasan Janbulo, sun bukaci matasa da su dai na yarda ana amfani da su yayin zabe

Kungiyar Janbulo Youth Forum ta yi kira ga matasa da su dai na yadda ‘yan siyasa na amfani dasu wajen ta da hankular jama’a domin biyan bukatun kansu na siyasa.

Sakataren kungiyar kwamared Abubakar Muhammad Sa’id ne ya bayyana haka, yayin wani gangamin wayar da kan matasa kan illolin tada hankulan jama’a da kungiyar ta gudanar jiya a yankin.

Ya ce wajibi ne al’umma da su sanya ido kan duk dan siyasar da su ka ga yana neman lalata tarbiyar matasa.

Wasu matasa da suka kasance a wajen taron sun bayyana irin darusan da suka koya a yayin taron.

Wakilin mu Bilal Nasidi Mu’azu ya rawaito cewa, kungiyar ta jaddada kudirinta na ci gaba da wayar da kan matasa dake lungu da sako na jihar Kano.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO