Kungiyar dattawan Arewa na kalubalantar dan takarar shugabanci na jam’iyyar PDP

Dan majalisar a jamhuriya ta daya kuma mamba a kungiyar dattawan Arewa Dr, Junaid Muhammed ya ce kungiyar ba ta amince da goyawa dan takarar jam’iyyar PDP Atiku baya ba a yayin babban zaben da za’a yi a ranar Asabar mai zuwa.

A cewar Dr, Junaidu wasu daga cikin ‘yan kungiyar dattawan Arewa ne wanda Ango Abdullahi ke jagoranta suke marawa dan takarar shugaban kasar baya ba duka ‘yan kungiyar ba.

 A dai makon da ya gabata ne wasi dattawan Arewa suka sanar da cewar za su marawa Atiku Abubakar baya a yayin zaben ranar 16 ga wannan watan na Fabarairu.

Hakan na ya biyo bayan taron da kungiyoyin dattawa suka gudanar a Abuja mai taken ‘’Taron shugabanni da dattawan Najeriya a inda kungiyoyin Ohaneze Ndigbo da Pan Niger Delta da Middle Belt da kuma tsagen kungiyar Afenifere suka yi don bayyana dan takarar da suke goyan baya.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO