Wasu yan bindiga sun kashe ma’ajin direbobin hanya ta kasa reshen Jibowu-yaba

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun kashe ma’ajin kungiyar direbobin hanya ta kasa reshen Jibowu-Yaba Alowonle Asekun  wata  makaranta dake Ikorodu dake jihar Lagos.

Rahotanni sun bayyana  cewar, ma’ajin kungiyar na kan hanyar sa ta zuwa wata makaranta a kan hanyar Ajasa-Lamberu, yayin da ‘yan bindigar suka harbe shi a ranar Juma’ar da ya gabata.

Wani ganau ya bayyana cewar, kashe ma’ajin kungiyar direbobin ya haifar da fargaba a zukantan al’ummar yankin Jibowu da kuma Fadeyi.

Haka zalika wani ganau Akeem Adepoju ya ce ‘yan bindigar sun harbi Asekun har sau 3 kafin mutuwar sa.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO