Gwamnatin Kano ta ce ta kashe Naira miliyan 128 wajen gyarawa da fadada cibiyar sauya hali dake Kiru

Gwamnatin Kano ta ce ta kashe Naira miliyan 128 wajen gyarawa tare da fadada cibiyar sauya hali dake yankin karamar hukumar Kiru a nan Kano.

Gwamnan jihar Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai ga gwamnan Aminu Kabiru Yassar ya sanya wa hannu cewa daga cikin kudin an gyara dakin kwanan dalibai da kuma wani bangare na maza.

Gwamnann ya bayyana hakan ne a yayin  da ake yaye daliban cibiyar fiye da dari 200 a karshen mako wanda na daya daga cikin sababbin tsaren-tsare wajen kawo karshen matsalar shan miyagun kwayoyi anan Kano.

Dr, Abdullahi Umar Ganduje ya nunar cewa, kafin ya kama mulki, an dakatar da ayyukan cibiyar wanda wasu kwararu ke kula da su.

Da yake jawabi shugaban kwamitin baiwa shugaban kasa shawara kan dakile shan miyagun kwayoyin a kasar Janaral Buba Marwa mai ritaya wanda ya sami wakilcin Kanal Yakubu Bako mai ritaya ya ce wasu daga cikin wadanda aka yaye a cibiyar marayu ne, yana mai nanata cewar don iyayen su bas a raye bai zama lalle a ce suna shaye-shayen miyagun kwayoyi Yayin da yake na shi jawabin shugaban hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa reshen jihyar Kano Dr, Ibrahim Abdul ya ce duk da cewar kididiga ya nuna cewar ana zargin jihar Kano ta fi ko’in a yawan masu shan miya gun kwayoyi a jihohin kasar na, hakan baya yana nuna cewar ba za’a iya yakar munmunar dabi’ar ba

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO