PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa a Kano

Jam’iyyar PDP ta ki amincewa da sakamakon zaben shugaban kasa da dan takarar Jam’iyyar Atiku Abubakar ya samu a Kano, wanda hukumar zabe ta kasa INEC ta sanar a jiya.

Wakilin jam’iyyar anan Kano, Rabiu Sulaiman Bichi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, kwata-kwata basu gamsu da sakamakon ba.

Alhaji Rabiu Suleiman Bichi ya kuma ce, ko a ranar zaben, akwai wurare da nau’rar tantance  masu kada kuri’a suka samu matsala yayin da a wasu mazabun an kada kuri’a fiye da adadin wandada na’ura ta tantance.

Share
Share
Language »