ACF:ta bukaci Atiku Abubakar da amince da sakamakon zaben shugaban kasa

Kungiyar dattawan Arewa ta ACF ta bukaci dan takaran shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da ya amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar ashirin da uku ga watan Fabrairu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran kungiyar Muhammed Ibrahim Biu.

Sanarwa da aka fitar da ita jiya a Kaduna, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasar da ya amince da zabin jama’a.

Kungiyar ta ACF ta cikin sanarwar dai ta kuma yabawa jajircewar Atiku da kuma kokarin da ya yi a yayin zaben, a don haka ta ce amincewa da sakamakon zai kara mishi mutunci a idon jama’a. Sanarwar ta kungiyar ACF ta ma buga misali da cewa ganin cewa an gudanar da zaben cikin lumana ba tare da samun tashin hankali masu yawa ba kuma kungiyoyin sanya idanu sun yaba da nagartar sakamakon, a don haka zai fi kyautatuwa Atiku Abubakar ya amince da sakamakon

Share
Share
Language »