Harin Zamfara: yan bindiga sun kashe mutane 13

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari kauyen Kawaya dake karamar Hukumar Anka a jihar Zamfara, inda suka kashe fiye da mutane 13.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’addar sun kuma kona gidaje da ababen hawa tare da yin garkuwa da mutanen fiye da 30.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar SP Muhammadu Shehu ya tabbara da faruwar al’amarin sai dai ya ce mutane 11 ne suka rasa rayukan su.

Ya kuma ce gamayyar jami’an tsaro na fadada bincike a dajin da ke kusa da kauyen da al’amarin ya auku don gano wadanda suka aikata wannan danyen aiki tare da gurfanar da su gaban kuliya don girbar abinda suka shuka.

Ya ce duk da cewa a yanzu al’ummar yankin sun koma cigaba da gudanar da al’amurran su na yau da kullum amma dai har yanzu akwai jami’an tsaro da ke sunturi a wajen.Share
Share
Language »