INEC SOKOTO:Gwamna Tambuwal ya ce basu amince da ayyana zaben jihar bai kammala ba

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Gwamnan jihar Sakkwato kuma dan takarar gwamnan jahar a karkashin jam’iyyar PDP, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, ya ce basu amince da ayyana zabe a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamnan na wadannan kalamai ne yayin taron gaggawa da manema labarai da suka gudanar tare da masu ruwa da tsaki a jihar da yammacin jiya Litnin.

Gwamna Tambuwal ya ce sun yi natsarin kundin tsarin mulkin kasa da na hukumar zabe amma basu ga inda aka bayyana wannan dokar da ta ce a ayyana wani zabe a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamna Tambuwal ya amsa cewa akwai dalilan da kan sa a soke zabe ta yadda ma ba za a sake yi ba; akwai kuma dalilan da kan sa a soke amma kuma a sake wani sabo. Ya ce to amma hukumar INEC ba ta alakanta daya daga cikin irin wadannan yanayi da ayyana zaben jahar Sokoto a matsayin mara kammala da ta yi ba.

Gwamna Tambuwal ya ce ta na yiwuwa su ruga kotu su kalubalanci ayyana zaben a matsayin mara kammala. Ya kuma yi nuni da cewa akasarin jahohin da aka ayyana zabensu a matsayin marasa kammala ‘yan takarar PDP ne ke kan gaba. Sannan ya yi hanunka mai sanda ga jami’an hukumar INEC da cewa idon duniya na kansu.

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO