Kano:An harbe mutane biyu tare da garkuwa da wani dan kasar Lebanon

AD INJECTION TEST ADVERT 728x90
Ad Injection
www.advancedhtml.co.uk

Masu garkuwa  da mutune sun harbe mutane biyu inda kuma suka yi garkuwa da wani dan kasar Lebanon ma’aikacin kamfanin Triacta dake aikin gina gadar dangi.

Lamarin dai ya faru ne da safiyar yau talata inda ake zargin masu garkuwa da mutanen sun zo a wata mota kirar golf da misalig karfe bakwai na safiyar yau talata suka kuma harbin iska don tarwatsa jama’a.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa wakilinmu Abba Isah Muhammad, cewa saida masu garkuwa da mutanen suka harbe ma’aikatan kamfanin biyu kafin dauke Mr Yalla Yaba wanda shi ma’aikacin da ake zargin anyi garkuwa da shi.

Sai dai koda muka tuntubi kakakin rundunar Yan Sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna, ta wayar hannu ya ce sun samu labarin faruwar lamarin kuma suna jiran bayanin baturen Yan sadan yanki da abun ya faru.

Wakilinmu Abba Isah Muhammad, da ya halarci gurin da lamarin ya faru ya ruwaito cewa alamuran aikin ya tsaya cik bayan faruwar lamarin.

=

AIM

TEST ADVERT 336x280 - reviewmylife

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO