Hukumar KAROTA zata ware jami’an da zasu kula da cinkoson Safiya da dare

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce, zata kara ma’aitanta a manyan titinan da ke fadin Jihar Kano da suka hadar da Dan Agundi da Hotoro dama wasu manyan titinan da nufin rage cinkoson da mutane ke kokawa akai yayin da suke kokarin komawa gidajen su.

Shugaban hukumar ta KAROTA Ibrahim Garba Kabara ne ya  bayyana hakan yayin zantawar sa da ya Freedom Radio a jiya Alhamis.

Ibrahim Garba Kabara ya ce  zasu raba sabbin ma’aitan da suka dauka ne zuwa guraren da ake kokawa  da yawan cinkoson ababen hawa locin fita wuraren ayyuka da kuma lokacin komawa gida.

Share
Share