0 Comments

Daraktan kwalejin kimiyya dake Dawakin Kudu Malam Abdullahi Musa Gezawa, ya bukaci masu hannu da shuni da sauran mutane da su himmatu wajen bayar da gudunmawa don ci gaban ilmi.

Malam Abdullahi Musa Gezawa ya bayyana hakan ne yayin bada kyaututtuka ga dalibai da malamai da suka yi hazaka a kwalejin.

Ya ce hukumar kwalejin tuni tayi shiri kan hanyoyin da za a dawo da cikakken tsarin koyarwar ilmin kimiyya ga dalibai.

Malam Abdullahi Musa Gezawa ya kuma kara da cewa, sashen jagoranci da nusarwa na kwalejin kimiyya ta Sani Bello dake Dawakin Kudu ya mai da hankali wajen gyara dabi’un dalibai don haifar da al’umma ta gari.

Da yake jawabi tun da faru, shugaban jami’ar Kimiyya da Fasaha dake garin Wudil Farfesa Shehu Alhaji Musa ya hori daliban da jajircewa kan karatun su, duba da ci gaban kowacce kasa ya ta’allaka ga ilmin kimiyya.

An fara amfani da sabon dakin kwanan dalibai mai cin mutane 80 da kungiyar tsoffin daliban kwalejojin kimiyya KASSOSA ta gina domin rage yawan dalibai a sauran dakunan kwanan su, da kuma samar da sabon masallaci tare da daukar gabaran gyara dakunan gwaje-gwajen na kwalejin da kungiyar ta dauki nauyi.

Share
Share
Language »