Joseph Yobo ya shawarci ‘yan wasan da za su wakilci Super Eagles a gasar cin kofin kasashen Afrika

Tsohon kyaftin din kungiyar kwallon kafa na Super Eagles Joseph Yobo, ya shawarci ‘yan wasa da za su fafata a gasar cin kofin kasashen Afrika su kasance masu jajircewa domin su taka rawan gani a wasan da za su buga a kasar Masar.

Yobo ya bayyan hakan ne yayin tattauna da manema labarai da safiyar yau Lahadi.

Tsohon kyaftin din ya kuma ce, ya kamata ‘yan wasan su hada kai don su samu sabon salon taka leda, wanda zai kai su ga nasara, tare da cewa, ko a zamaninsa sun bada gudunmowa wanda har ta kai ga sun samu nasara a wasani daban-daban.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO