Hukumar jin dadin alhazai ta yiwa maniyyata hajjin bana na Kaduna 2,200 gwajin daukar bayanai

Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kaduna ta yiwa maniyyata aikin hajjin bana 2,200 gwajin daukar bayanai ta hanyar dangwalen yatsa domin gudanar da aikin hajjin na bana.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar Yunusa Abdullahi ne ya sanar da hakan ga manema labarai lokacin da yake bayar da bayanan halin da hukumar ke ciki jiya Asabar a jihar Kaduna.

Rahotanni sun yi nuni da cewa zuwa Yanzu maniyyata 2,200 aka tantance a cikin adadin gurbin da aka baiwa jihar na maniyyata 6,636 a bana.

Yunusa Abdullahi ya ce, an fara daukar bayanan maniyyatan ne kwanaki uku da suka gabata kuma an fara da wuri saboda hakan zai taimaka gaya wajen dakile cinkoso.

Ya kara da cewa daukar bayanan mahajjatan ta na’ura mai kwakwalwa wani bangare ne da hukumar kasar Saudiyya ta ayyana shi a matsayin dole ga dukkan maniyyacin da zai halarci kasar domin suke farali.

Share
Share