RIPAN: An yi fasakwaurin shinkafa cikin kasar nan da ya kai sama da tan Miliyan daya

Kungiyar masu noman shinkafa ta kasa (RIPAN) ta ce cikin watanni uku da suka gabata an yi fasakwaurin shinkafa zuwa cikin kasar nan da ya kai sama da Tan miliyan daya.

Shugaban kungiyar ta kasa Muhammed Maifata ne ya bayyana haka yayin zantawa da menama labarai jiya a Abuja.

Ya ce masu zuba jari a bangaren noman shinkafa sun yi namijin kokari wajen zuba jari a bangaren sai dai suna fuskantar kalubale daga wajen masu fasakwaurin shinkafa daga ketare.

Muhammed Maifata ya ce akwai damuwa matuka ganin yadda wasu suka dage don ganin sun kawo koma baya, ga yunkurin samar da yalwataccen shinkafa ga al’ummar kasar nan, wanda cikin watanni uku kacal aka yi fasakwaurin buhu miliyan ashirin.

Shugaban kungiyar ta RIPAN ya kuma ce masu zuba jari a bangaren suna ta rufe kamfanonin su sakamakon rashin cin riba da su ke yi, wanda kuma hakan na alaka ne da zagon kasa da masu fasakwaurin shinkafa ke yi.

Share
Share