Farfelar jirgin saman rundanar sojin kasar nan ya fille kan want hafsan sojin sama

Farfelan jirgin shalkwabta mallakin rundunar sojin sama na kasar nan ya felle kan wani hafsan sojin sama a garin Bama da ke jihar Borno.

Rahotanni sun ce sojan mai suna Umaru Ganimu ya na cikin tawagar jirgin da ke yaki da mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas.

Shaidun gani da ido sun ce Umaru Ganimu ya zo wucewa ta kusa da farfelan jirgin da ke kunne wanda sanadiyar hakan farfelan jirgin ya fille mashi kai.

Kuma tuni aka yi jana’izar sa a makabartar barikin soji ta Maimalari da ke Maiduguri a jihar ta Borno.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO