0 Comments

Jiragen yakin rundunar sojin sama na kasar nan sun yi luguden wuta kan wasu maboyar ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin jiragen yaki guda takjwas da aka tura jihar ta Zamfara domin fatattawar ‘yan bindigar sun kai hare-hare ciki kuwea da har da wata makarantar firamare da ake zaton ‘yan bindigar sun mai da shi gida.

Wani shaidan gani da ido ya shaidawa manema labarai cewa jiragen yakin sun yi kazamin barna ga ‘yan bindigar wadanda suke samun mafaka a ginin makarantar.

Haka zalika ya tabbatar da cewa tuni jama’a suka fara amfani da titin da ya hada jihohin Zamafar da katsina wato titin Kaura Namoda zuwa Zurmi zuwa Jibia sakamakon fatattakar ‘yan bindiga da sojoji da sauran jami’an tsaro su ka yi a yankin.

Rahotanni sun ce an samar da wata cibiyar da jiragen yakin run dunar sojin saman kasar nan  za su rika sauka suna shan mai a garin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna maimakon komawa garin Kaduna ko Abuja lamarin da ya taimaka gaya wajen daukar mataki akan lokacin.

 

Share
Share
Language »