0 Comments

Rundunar sojin saman Najeriya ta ce ba gaskiya bane cewa hare-haren da jiragen yakin ta ke kaiwa a jihar Zamfara yana karewa ne akan fararen hula.

Mai magana da yawun rundunar Air Commodore Ibikunle Daramola ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Alhamis, ya ce zance ne kawai maras tushe da bashi da makama.

Sanarwar ta kuma ce rundunar sojojin saman ta  barranta kanta da wani labari na karya da ake ta yadawa a kafafen sada zumunta cewa jiragen yakin dakaratun ‘’OPERATION DIRAR MIKIYA” sun kashe fararen hula ne maimakon ‘yan bindiga a ci gaba da hare-hare ta sama da suke kai wa a jihar Zamfara.

A cewar Air Commodore Ibikunle Daramola a cikin sanarwar dai hare-haren da suke kaiwa suna kaishi ne kawai a yankunan da suka yi kaurin suna da ayyukan ‘yan bindiga mafi yawansu ma fararen hula ba sa zama a yan kunan.

Air Commodore Ibikunle Daramola ya ce hare-haren ta sama an kai su ne a dazukan Rugu da Sububu da kuma Kagara yankunan da kwara-kwata babu fararen hula maboya ne na ‘yan bindiga.

Mai Magana da yawun rundunar sojin saman ya kuma ce ba sa kai hari sai sun samu cikakken rahoton sirri, kafin su ke daukar mataki.

Share
Share
Language »