Kungiyar ICRC ta horas da Fulani dabarun kula da dabbobi

Sarkin Rano Alhaji Tafida Abubakar ya ce, akwai bukatar masu rike da sarautun gargajiya su hada hannu da shugabannin makiyaya domin dakile rikici tsakanin makiyaya da manoma.

Alhaji Tafida Abubakar ya bayyana hakan ne yayin bikin yaye makiyaya 30 da suka samu horo kan dabaru da hanyoyin bada agaji ga lafiyar dabbobi wanda kungiyar agaji ta ICRC ta dauki nauyi.

Da yake jawabi yayin taron, shugaban kungiyar a jihar Kano Ahmad Awadalla ya ce, an shirya horaswar ne domin koyar da Fulani yadda za su kula da dabbobin su da kuma dakile matsalolin yada cutuka daga dabbobi zuwa mutane.

Wasu daga cikin Fulani da suka ci gajiyar horaswar sun bayyana cewa za su yi amfani da ilmin wajen ciyar da al’ummar su gaba ta fannin kula da lafiyar dabbobin su da kuma bunkasa sana’ar kiwo.

Share
Share