0 Comments

Daya daga cikin Dattijan Naheriya Malam Abdurrahman Umar Dikko ya ce, amfani da manyan bindigu da ‘yan ta’adda ke yi wajen aikata ta’asa a kan manyan titunan jihohin Arewacin Najeriya abu ne mai matukar tada hankali tare da yin sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama.

Malam Abdurrahman Umar Dikko, ya bayyana hakan ta cikin shirin ‘Mu leka Mu Gano’ na musamman na Freedom Radio, wanda ya mayar da hankali kan lalubo hanyoyin da za a dakile matsalolin tsaro da ke addabar yankin Arewacin Najeriya.

Dattijon ya kara da cewa akwai bukatar mahukuntan su mayar da hankali wajen sintirin jami’an tsaro a manyan titina maimakon sanya shingayen bincike wanda a lokuta da dama batagarin ke kafa nasu shingen tare da sanya kayan sarki ta yadda mutane zasu dauka jami’an tsaro ne.

Haka kuma ya  ce, ko lokutan baya an samu makamanciyar wannan matsala, sai dai mahukuntan wancan lokaci sun samu nasarar shawo kanta cikin sauki sakamakon irin matakan da suka dauka.

Malam Abdurrahman Umar Dikko,  ya ce, abun takaici ne yadda ‘yan ta’addar ke amfani da manyan makamai wajen tare mutane inda suke kashe mutane babu gaira ba sabar.

Share
Share
Language »