0 Comments

Mai rikon mukamin daraktan ayyukan na hukumar tace fina-finai ta kasa NFVCB Mrs Bola Athar ta ce hukumar ta kwace fina-finan batsa da wasu su Karin fina-fian da bata bayyana ba, da kudin sa ya tassama fiye da Naira biliyan 2 cikin shekaru 2.

 

Mrs Bola Athar ta bayyana hakan ne a yayin da manema labarai ke ganawa da ita a daren jiya Lahadi yayin bikin cikar babban darkatan hukumar Mr Adedayo Thomas da ya cika shekaru 2 a hukumar wanda aka yi a Abuja.

 

Rahotanni sun bayyana cewar kososhin gwamnarti da masu ruwa da tsaki a fina-finai sun halacci liyafar cin abincin daren, saboda gudunmawar da Mr Adedayo Thomas ya bayar ga cigaban masana’antun shirya fina-finai ta kasa cikin shekaru 2 da kama aikin sa.

 

A cewar Mrs Bola Athar daga cikin fina-finan akwai na batsa da na kasashen waje da kuma kayayyakin aiki da suka hada DVD, da kwafin fefen bidiyo mai kunshe da fina-finai guda 20 cikin CD guda.

Share
Share
Language »