Ministan yada labarai yace gwamnatin Buhari zata yaki cin hanci da rashawa

Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohamme ya baiwa ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje tabbaccin  cewar sabowar gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari zata sake daura zani wajen yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.

 

Alhaji Lai Mohmmed ya bada tabbacin ne a yayin da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan jawabi ga ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, cewa sabuwar gwamnatin ba zata yi wasaraire da shirin yaki da cin hanci da rashawa da kuma manufofin ta ba wajen cigaban kasar nan.

 

Rahotanni sun bayyana cewar ministan ya bayyana hakan ne a birnin Washington D.C yana mai sake jadada nasarorin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu cikin shekaru 4 da suka gabata.

 

Yayin da yake ganawa da manema labarai don karfafa dagantakar Najeriya da manema labarai dake kasashen ketare, Lai Mohammed  ya ce gwamnati mai ci na kokarin magance matsalar tsaro da ta addabi wasu sassan kasar nan.

Share
Share