DSS:ta sako magoya bayan akidar Kwankwasiya su biyu

Hukumar tsaron sirri ta DSS ta sako daya daga cikin magoya bayan akidar siyasar Kwankwasiyya mai suna Salisu Hotoro da Babangida da akewa lakabi da Bangis wadanda ta kama a kwanakin baya, bayan sun kwashe tsawon kwanaki goma sha biyu.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun dan takarar gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar PDP Sanusi Bature Dawakin-Tofa.

 

Sanarwar ta ce jami’an hukumar tsaron sirri ta DSS ne suka kama mutanen biyu makwanni biyu da suka gabata, bisa zargin da su kansu ba a sanar da su ba.

 

A cewar sanarwar, sakamakon rashin hujjoji da hukumar ta DSS ke da shi kan mutanen biyu, ya sanya ta gaza gurfanar da su gaban kotu.

 

Sanusi Bature Dawakin-Tofa ta cikin sanarwa dai, ya kara da cewa, jam’iyyar PDP, za ta zauna don daukar mataki na gaba game da shirin ta na gudanar da zanga-zangar lumana a gobe Alhamis, wanda ta shirya tun da fari za ta yi, da nufin nuna adawa da cin zarafin ‘ya’yan jam’iyyar da jami’an tsaro ke yi a jihar Kano.

Opinion Polls

Listen – iOS

Tune In

Share
Share
  • Hukumar kiyaye hadurra a Najeriya ta kama motocin sata 70 a wasu jihohin kasar
  • zamu sake nazartar sayar da kadarorin da suka shafi bangaren lantarki-Shugaba Buhari
  • kasar Isra’ila zata fice daga hukumar UNESCO