Dakarun kasa da kasa sun kashe mayakan boko haram 39

Abubakar Shekau

Dakarun kasa da kasa da ke aikin samar da tsaro a yankin arewa maso gabashin kasar nan sun kashe mayakan  Boko haram guda talatin da tara, a yayin wata gwabzawa da su ka yi a baya-bayan nan.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun dakarun hadakar kanal Timothy Antigha.

 

Sanarwar ta ce sojojin sun kuma kwato wasu nau’ikan makamai daga wajen ‘yan ta’addar, yayin da kuma wasu sojoji ashirin suka samu munanan raunuka.

 

Sanarwar ta ce sojojin sun kashe ‘yan ta’addar ne lokacin da su ka yi yunkurin kai musu hari a wani sansaninsu da ke Kaura, a shekaran jiya Talata.

 

Kanal Timothy Antigha ya kuma ce tuni aka garzaya da sojojin da suka samu raunukan zuwa asibiti domin kula da lafiyar su.

 

Share
Share