Freedom Radio Nigeria Labarai CBN: zai janye kudaden da suka lalace daga hannu jama’a

CBN: zai janye kudaden da suka lalace daga hannu jama’aBabban bankin kasa CBN ya ce zai janye kudade da su ka lalace daga hannun jama’a, wadanda yawansu ya kai kusan naira tiriliyan takwas.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin gwamnan babban bankin kasa CBN Folashodun Shonubi da kuma daraktar kudi na babban bankin Mrs Priscilla Eleje.

Sanawar ta ce kudaden sun yi lalacewar da na’urorin ciran kudi na banki wato ATMs basa iya gudanar da hada-hada da su.

A cewar sanarwar, a gobe talata, gwamnan babban bankin kasa CBN Godwin Emefiele zai kai ziyara Lagos don kaddamar da sabon tsarin sabbin takardun kudi.

Bankin na CBN ya ce wannan wata hanya ce ta dakile lalacewar takardun naira.