Freedom Radio Nigeria Kiwon Lafiya Kaduna: rundunar yan sanda ta Kama wani da ake zargin yana da hannu a kashe basaraken Adara

Kaduna: rundunar yan sanda ta Kama wani da ake zargin yana da hannu a kashe basaraken AdaraRundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta kama wani mutum da ake zargi yana da hannu a kashe basaraken kasar Adara Maiwada Galadima a kwanakin baya, a jihar ta Kaduna.

 

A dai watan Oktobar shekarar da ta gabata ne aka kashe basaraken kasar ta Adara Maiwada Galadima akan hanyar sa ta dawowa gida, bayan ya raka gwamna Nasir El-rufai zuwa kasuwar Magani don yin jaje ga wadanda rikicin yankin ya shafa.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai Magana da yawun rundunar ‘yan sandan kasar nan DCP Frank Mba.

 

Sanarwar ta ce, mutumin mai suna Abubakar Ibrahim da akewa lakabi da Dan Habu mai shekaru talatin da bakwai, dan asalin yankin karamar hukumar Igabi ne da ke jihar ta Kaduna.

 

A cewar DCP Frank Mba mutumin ya amsa da bakin sa cewa shi mai satar mutane yana garkuwa da su ne, kuma shine ya kashe basaraken kasar ta Adara Maiwada Galadima