Freedom Radio Nigeria Labarai UBEC:an yi garkuwa da shugaban hukumar Muhammad Mahmood tare da diyarsa

UBEC:an yi garkuwa da shugaban hukumar Muhammad Mahmood tare da diyarsaRundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da sace shugaban hukumar kula da ilimin bai daya (UBEC) Muhammad Mamood tare da ‘yar sa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar ta Kaduna, Yakubu Sabo.

 

A cewar sanarwar, da misalin karfe uku da mintuna talatin na yammacin jiya ne ‘yan bindiga suka sace shi da ‘yar sa.

 

Mai magana da yawun ‘yan sandan na jihar Kaduna ya kuma ce masu satar mutane suna garkuwa da su, sun kuma kashe direban shugaban hukumar ta UBEC.

 

Wani faifan bidiyo da aka yada a kafar sada zumunta ta Intetnet, ya nuno wani mutum kwance cikin jini a gefe guda kuma ga jami’an tsaro da masu wucewa.

 

Sanarwar ‘yan sandan ta kara da cewa, ‘yan bindigar suna sanye ne da rigunan sojoji, kuma sun tare mutanen ne a kauyen Kurmin Kare.